WASHINGTON D.C. —
Fitaccen zakaran kulab din PSG Neymar baya jin dadin wasa a Faransa, kuma ya matsu da ya koma zuwa Barcelona don ci gaba da buga wasa.
An bada rahotonnin dan wasan kasar Brazil din bai ji dadi da irin matsalolin kungiyarsa ba, a fagen wasannin zakarun turai na European.
Ya kuma yi imanin da cewar komawa tsohuwar kungiyarsa yana da dama mai kyau na lashe kofin zakarun turai.
Sai dai an fitar da PSG a gasar a zagaye na 16 a duk kakar wasanni biyu da Neymar yayi a kulab din.