Dan Najeriya Ya Samu Lambar Yabo A Abu Dhabi

Lokacin da aka sanar da AbdulLateef Olaosebikan a matsayin wanda ya lashe lambar yabo a Abu Dhabi

Kamfanin na Olaosebikan ya doke ABOLOBI na Afirka ta Kudu da Xinjiang Shawan Oasis na kasar China a gasar.

AbdulLateef Olaosebikan ya lashe lambar yabo a gasar ZAYED ta samar da ci gaba mai dorewa a duniya da ke wakana a Abu Dhabi a Hadaddiyar Daular Larabawa.

Olaosebikan ya karbi kyautar ne karkashin kamfaninsa na NaFarm Foods da ke jihar Kadunan Najeriya wanda ya shiga gasar a rukunin kamfanonin da ke samar da abinci ta hanyar amfani da tsabtataccen makamashi.

NaFarm ya yi fice ne a fannin busar da abinci ta hanyar amfani da makamashin hasken rana.

Kamfanin ya doke ABOLOBI na Afirka ta Kudu da Xinjiang Shawan Oasis na kasar China.

“Abin da Najeriya ke bukata shi ne mutane irinmu da suke kokarin amfani da fasahohin zamani wajen samar da abinci da adana shi wanda hakan na yi ammar zai taimaka wajen samar da abinci mai dorewa.” Olaosebikan ya ce a wata hira da manema labarai wacce Ministan Harkokin wajen Najeriya Yusuf Maitama Yusuf Tuggar ya wallafa a shafinsa na X.

Minista Tuggar ya taya Olaosebikan murnar lashe wannan kyauta.

“Muna taya NaFarm Foods, wani kamfani daga Jihar Kaduna a Najeriya, murna kan samun lambar yabo ta “ZAYED Sustainability Prize” a rukuni na abinci a Abu Dhabi na 2025.” In ji Tuggar.

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu na daga cikin shugabannin kasashen da ke halartar taron daga nahiyar Afirka.