Dan Kunar Bakin Wake Ya Hallaka Masu Zanga-Zanga 61 a Kabul

Wata Mata Na Kuka Bayan Harin Kunar Bakin Waken Da Aka Kai a Kabul, Afghanistan Yuli 23, 2016.

Wani katafaren bam ya tarwatse a tsakiyar masu zanga-zanga a Kabul babban birnin kasar Afghanistan, wanda Kakakin ma’aikatar lafiya na kasar yace akalla mutane 61 ne suka mutu.

Kakaki Mohammad Isma’il Kawasi ya fadawa Muryar Amurka cewa, wasu mutanen akalla guda 207 sun jikkata a wannan mummunan harin. Abin ya faru ne a lokacin da ‘yan kabilar Hazaras ke macin neman cewa gwamnati ta karkato da akalar digar jirgin kasa ta cikin unguwarsu.

Unguwar da take fama da talauci da ke tsakiyar lardin Bamiyan. Shedun gani da ido da ‘yan jarida sun rawaito yadda suka ganewa idanunsu gawarwaki a wajen da fashewar bam din ta faru.

Jjami’ai kuma sun ce akwai yiwuwar karuwar yawan mamatan. Harin dai ya yi kama da cewa wani dan kunar bakin wake ne ya tada kansa a cikin dandazon jama’ar masu zanga-zangar.

Shugaban kasar Ashraf Ghani yace harin ta’addanci ne, shi kuma Kakakin Taliban Zabihullah Mujahid yace ba ruwansu a wannan lamari.