Dan Jarida: "Rediyo Ne Uwa Sha Da Mama"

Ranar Rediyo

Ma'abota Sashen Hausa sun bayyana ci gaban da aka samu da ke ba kowa damar sauraron radiyo, da suka hada da amfani da yanar gizo da kuma wayoyin hannu da aka fi sani da salula.

Ma'aikan gidan Rediyo da kuma masu sauraro sun ce Radiyo na da muhimmanci da kuma tasiri da zai iya hada kan mutane ko kuma zama sanadin rarraba kawunansu.

A cikin hirar da Sashen Hausa ya yi da wadansu masu saurare, sun bayyana cewa, rediyo ne hanya mafi sauki na samun labarai daga kusurwowi daban daban.

Rediyo na samar da labarai, ya ilmantar ya kuma nishadantar. Muhimmancin Radiyo ga al'umma ya sa babban taron majalisar dinkin duniya a 2012 ya ayana ranan 13 ga watan Fabrairu a matsayin ranan rediyo na duniya.

Wakilin Muryar Amurka, ya ji ta bakin wadansu masu sauraron radiyon wadanda suka bayyana cewa, rediyo na taimakawa wajen ilmantar da al'umma, da sanar da su abubuwan da ke faruwa a duk fadin duniya.

A saurari cikakken rahoto cikin sauti daga babban birnin Accra a Ghana.

Your browser doesn’t support HTML5

'Dan Jarida: "Rediyo Ne Uwa Sha Da Mama"