WASHINGTON, DC —
Dogaro da kai shine abun da ya kamashi mata inji Adama Umar, wata mai sana'ar sayar da abinci, a birnin Kano, tace ta kwashe shekaru bakwai tana sana'ar sayar da abinci domin tabbatar da ganin cewa 'yan'yan ta sun samu ilimi.
Ta kara da cewa sana'ar tana taimakamata waje tafiyar da harkokin ya'u da kullum domin a cewar ta tsufa ya kama mijinta, wanda yaza dole ta tashi tsaye domin taimakawa, "Dan guntun gatarinka yafi sari kabani."
Malama Adama , ta ja hakalin 'yan uwanta mata, dasu daina rena sana'a, su tashi su nemi na kansu domin samun biyan bukata ba a kowani lokaci su kasance masu 'yar muryar ba ka 'yan uwa domin samun biyan bukata.