Dan Guntun Gatarin Ka - Inji Fiddausi Mai Karamar Sana'a

Fiddausi Auwal Idris

Fiddausi Auwal Idris, daga karamar hukumar Dawakin Tofa-ta ce kananan sana’oin da mata kan raina saboda kankancinta ne kan haifar da babban jari har ta kai ga an sami amfanin ribar sana’a.

Fiddausi dai ta bayyanawa wakiliyar Dandalinvoa cewar tana sayar da kayan alewa ta yara domin tafiya da su makaranta, ta tara riba mai yawa har ta kai ta ga ta fara kiwo.

Ta ce, ta shafe kusan shekaru bakwai Kenan tana sana’ar dogaro da kai domin tabbatar da cewar dukkanin wasu kananan bukatu ta fi karfinsu, kuma ta kauda yawan bani-bani da mata kan yi wa iyaye ko mai gida.

Ku Duba Wannan Ma Aure Baya Hana Neman Ilimi - Dr Maryam Sani Ado

Fiddausi ta ce wasu lokutan ana biyo ta gida domin a sayi kayan da take sayarwa wata sa’ar kuwa tana dorawa yara kayan tande-tande domin su kai makaranta su sayar da zarar an fito hutun tara, kokuma kafin ma a shiga aji.

Daga karshe ta ce duk kuwa da cewar karamar sana’a ce, yin hakan bai hana ta fuskantar kalubale ba doin kuwa idan ta dorawa yara, akan ci rashin sa’ar samun dalibai masu cin zali da zasu dauki bashin alewa su kuma ki biyan kudi.

A cewar ta dai babban burinta shine ta bude ‘yar tireda domin kasa kayanta na sayarwa.

Your browser doesn’t support HTML5

Dan Guntun Gatarin Ka - Inji Fiddausi Mai Karamar Sana'a