A Nijar An Kirkiro Gasa Tsakanin Makarantun Firamari Domin Inganta Ilmi

Malaman Makarantun firamari a Nijar

Gasar da mahukumtan harkokin ilmin firamari suka kirkiro a jihar Damagaran ta taimaka gaya wajen inganta ilimin firamari da na yaki da jahilci

Shugaban hukumar dake kula da makarantu firamari a jihar Damagaran ya e an shirya gasar ce tsakanin makarantun firamare don daga kananan yara har zuwa kan yara manyan.

Cikin fannoni da za'a yi gasar harda Hausa, tatsuniya da tarihi na Damagaran akwai kuma kere kere da fasaha.

Kowace makaranta zata kirkiro abubuwa biyu ta mikawa mahukumta. Wannan zai sa yara su kara hazaka.

Gasar ta kunshi tambayoyi 500 da suke karawa yara kuzari.

A cewar jagorar kananan makarantu Madam Ali Halima ta ce, shiyya ta uku zata taimakawa karatun yaran gaya, saboda shirin na inganta ilmi da kara zurfafa ilimi domin yara suna kara bincike bisa abubuwan da su keyi a makarantunsu.

Shirin yaki da jahilci ma ba'a barshi a baya ba, domin su ma akwai irin tasu gasar.

Ga rahoton Tamar Abari da karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

Damagaran A Nijar Ta Kirkiro Gasa Tsakanin Makarantun Firamari Domin Inganta Ilmi - 2' 42"