Fitaccen malamin addinin Islama a Najeriya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya ce dalilin da ya sa suka yi hawan Idin Karamar Sallah a ranar Laraba shi ne, sun samu tabbacin ganin watan Shawwal.
“Idan wata bai buya ba an gan shi, to mene ne uzuri, kuma ba mu da ikon mu karyata wadanda suka ce sun ga watan.” Sheikh Dahiru ya ce.
Ya kara da cewa, “an gani a nan Bauchi, na ga mutumin ma, an gani a Gombe, an gani a Gadau, an gani a Arugungu an kuma gani a Zamfara.”
A ranar Talata Majalisar da ke kula da al’amuran addinin Islama a Najeriya ta NSCIA, wacce ke karkashin jagorancin Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Sultan Saa’d Abubakar, ta ayyana cewa za a yi Sallah ne a ranar Alhamis 13 ga watan Mayun 2021.
Karin bayani akan: Sheikh Dahiru Usman Bauchi, Eid-al-Fitr, Islama, Sallah, Nigeria, da Najeriya.
Majalisar ta ce, ta dauki wannan matsaya ce saboda ba a ga watan Shawwal a ranar Talata ba.
“Saboda haka, za a yi azumi na 30 a ranar Laraba 12 ga watan Mayu 2021, hakan na nufin Alhamis 13 ga watan Mayu, ya zama 1 ga watan Shawwal 1442 kuma ranar Sallar Eid-al-Fitr.” Sanawar NSCIA ta ce a shafinta na Twitter.
Da misalin karfe bakwai na safiyar ranar Laraba, mabiya darikar Tijjaniya daga ciki da kuma wajen Birnin Bauchi, suka yi tururuwa zuwa gidan Shehin Malamin domin gabatar da Sallar Eid-al-Fitr da aka gudanar da misalin karfe tara da 9:30.
Sallar ta gudana ne karkashin jagorancin Liman Malam Ahmed Tijjani Tahir Usman Bauchi.