PLATEAU, NIGERIA - A makon jiya ne rundunar ‘yan sandan ta Jihar Filato ta cafke wasu matasa 13 a wani kogon dutse a yankin Down Base da ke karamar hukumar Jos ta Arewa.
A wata sanarwa daga jami’in huldar jama’a na rundunar ‘yan sandan ta Jihar Filato, DSP Alfred Alabo, ta ce kogon dutsen da ta kama matasan wuri ne da matasa ke gudanar da ayyukan asiri, shaye-shaye da sauran ayyukan da ba su dace ba.
Matasan sun karyata zargin da ake musu inda suka ce sun je wurin ne don atisayen hawan dutse.
Madam Christiana Jankam da ke zaune a yankin na Down Base ta ce a kowane mako sai an yi garkuwa da mutane biyu zuwa uku dalilin da ya sa ake maida hankalin da irin wadannan ayyukan.
Malam Yusuf Abdullahi Wase ya ce dole sai al’umma sun hada kai da jami’an tsaro don samun mafita.
Rundunar ‘yan sandan dai ta ce za ta gurfanar da matasan 13 a gaban kuliya, saboda sun hau dutsen ne ba tare da sun shaida wa shugabannin al’umma na yankin ba.
Saurari rahoto cikin sauti daga Zainab Babaji:
Your browser doesn’t support HTML5