Hukumar da ke kula da kafafen yaɗa labarai a Najeriya NBC, ta haramta waƙar “Warr” wacce fitaccen mawakin Hausa Ado Gwanja ya rera.
A ranar 30 ga watan Mayun 2022 Gwanja ya saki sautin wakar ta “Warr” ya kuma fitar da bidiyonta a ranar 1 ga watan Agusta.
Cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba mai taken “Damuwa kan wakar Ado Gwanja ta Warr,” hukumar ta NBC ta ce wakar na dauke da wasu kalamai da ba su dace ba, sannan bidiyonta na kwadaitar da halayya ta maye idan mutum ya sha barasa.
“Hukumar ta damu, duba da yadda wakar ta samu karbuwa a wajen wasu kafafen yada labarai a yankin, abin da ke nuni da cewa tashoshin ba su zauna sun saurari abin da ke cikin wakar ba kafin su watsa ta.” Sanarwar wacce reshen hukumar ta NBC na Kaduna ya fitar ta ce.
Hakan na nufin ba za a sake saka wakar a wani gidan rediyo ko talabijin ba a Najeriya.
Hukumar wacce ta yanko wasu daga cikin baitukan da take kalubalanta, ta ce, sakonnin da wakar ke dauke da su, sun sabawa dokokinta.
“Hotunan bidiyon wakar, ya nuna karara yadda ake shan barasa, wanda hakan ya sabawa dokokin watsa labarai ta hukumar, wacce ke kunshe a sashe na 3.18.2 (C) da sashe na 3.9, wadanda suka bukaci duk wata kafar yada labarai ta kasance mai nuna sanin ya kamata kan duk wani abu da za ta watsa.
Mutum miliyan 1.1 ne suka kalli wakar cikin wata daya, kana miliyan 1.7 suka saurari sautinta a kafar YouTube cikin wata uku.