Dalilin Da Ya Sa Ake Samun Layukan Mai A Wasu Biranen Najeriya - NNPC

Hedikwatar NNPC

An samu dogayen layukan man fetur a wasu manyan biranen Najeriya a ranar Litinin bayan da kamfanin mai na NNPC ya fuskanci matsalar samar da mai ga ‘yan kasuwa da gidajen man fetur na cikin gida.

A shekarar da ta gabata ne gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta bude wa kamfanoni masu zaman kansu shigo da mai amma karancin kudin kasashen waje da kayyade farashin man fetur ya sa kamfanin NNPC ya kasance shi ka dai ne mai shigo da mai.

Sabuwar matatar mai ta Dangote har yanzu ba ta fara sarrafa man fetur ba.

ABUJA: NNPC

“Hukumar NNPC Ltd na son bayyana cewa matsi da aka samu wajen raba man fetur da aka samu a wasu sassan Legas da babban birnin tarayya ya biyo bayan cikas ne da ake samu na fitar da mai daga wasu hanyoyin guda biyu,” Olufemi Soneye, mai magana da yawun kamfanin NNPC ya ce a wata sanarwa a karshen mako lokacin da aka fara yin layuka.

Malam Mele Kyari Shugaban NNPC

Farashin mai dai a gidajen sayar da man fetur ya haura sama da Naira 800 daga kusan Naira 617 a kowace lita a watan Mayun 2023 lokacin da gwamnati ta sanar da kawo karshen tallafin mai. Hauhawar farashin dai ya kara haifar da hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya da kuma tsadar rayuwa.

Dillalan man fetur dai na bin kamfanin NNPC Ltd sama da dala biliyan 6, wanda hakan ya shafi kayayyaki, kuma kafanın dai yana neman samun kudade don daidaita basussukan.

-Reuters