Dalilin Da Ya Sa Aka Kasa Shawo Kan Matsalar Tsaro A Arewacin Najeriya - Masana

Zanga-zangar Nuna Takaicin Rashin Tsaro A Jihar Nejan Najeriya

A cewar masanan, muddin ba a sauya salon yadda ake tafiyar da shari'ar wadanda ake zargi da laifukan ba, hakan zai yi ta mayar da hannun agogo baya.

A Najeriya yaki da ‘yan ta'adda da hukumomi ke yi wasu lokuta jami'an tsaron na samun galaba, sai dai abin tambaya shi ne me ya sa ta'addancin yaki raguwa duk da nasarar da hukumomi ke samu.

Tun lokacin da ayukkan ta'addanci suka fara addabar ‘yan Najeriya, mahukumta suka daura damarar fada da munanan ayukkan, amma dai ayukkan sai kara bazuwa suke yi a sassa daban-daban.

Baya ga hallaka ‘yan ta'addar da ake yi wasu lokuta duk da yake su ma suna samun sa'ar jami'an tsaro, haka ma ana kama su a tsare kamar yadda ya faru a Sokoto inda jami'an tsaron ‘yan kasa na Civil Defence suka damke mutane 11 da ake zargi da hannu da satar mutane, da satar dabbobi da ma masu kaiwa barayin kayan abinci.

“Mun kama ‘yan ta’adda barayin shanu mutum bakwai, wadannan da muka same su sun tabbatar mana da cewa suna da hannun a kashe-kashen da aka yi da satar mutane.” In ji Muhammad Sale Dada, kumandan hukumar a Sokoto.

Wasu daga cikin wadanda aka kaman sun aminta da laifukan da ake tuhumar su, lokacin da na zanta da su.

Wannan dai ba shi ne karon farko da ake kama ‘yan ta'addar ba, amma daga hakan ba za'a sake jin komai ba, abi nda masu sharhi akan lamurran yau da kullum ke kallo a zaman gurbacewar ‘yan kasa ne ke kawo hakan tamkar yadda Dr. Usman Abdulkadir na sashen nazarin halayyar Dan Adam a jami'ar Usmanu Danfodiyo ya bayyana.

“Abu ne kamar hadaka, za ka ga akwai jami’an tsaro akwai alkalai akwai Sarakuna, sai ka ga mutum ga shi mai laifi amma sai ka ga lauyoyi suna kare shi.” In ji Dr Abdulkadir.

Malamin dai na ganin muddin ba canja halaye ‘yan kasa suka yi ba, tare da saka kasa gaba ga bukatun kansu ba to ba za'a fita daga irin wannan yanayin ba.

Saurari cikakken rahoton Muhammad Nasir daga Sokoto:

Your browser doesn’t support HTML5

Dalilin Da Ya Sa Aka Kasa Shawo Kan Matsalar Tsaro a Arewacin Najeriya - Masana - 3'02"