A Jamhuriyar Nijar wasu kungiyoyi masu zaman kansu sun karrama jakadan Najeriya a Nijar sakamakon lura da abin da suka kira ‘’rawar da ya taka wajen ganin an farfado da hulda a tsakanin gwamnatocin kasashen biyu wadanda suka shiga zaman ‘yan marina a sanadiyar juyin mulkin 26 ga watan yulin 2023.
Jerin takunkumin da ECOWAS ta kababa wa Nijar da barazanar amfani da karfin sojan da kungiyar ta ayyana don mayar da hambararren shugaban kasa kan kujerarsa su ne musabbabin yanayin tsamin dangantakar da aka shiga a tsakanin Najeriya da Nijer.
Lura da rashin dacewar faruwar wannan al’amari a tsakanin wadanan kasashe da tun fil azal ake kiransu Dan Juma da Dan Jumai ya sa jami’an diflomasiya suka dage da tuntubar bangarori domin warware zaren rikicin da ya sarke kuma a cewar gamayyar kungiyoyin hadin kan al’umomin Najeriya da Nijar jakadan Najeriya na kan gaban wadanda suka yi rawar gani a yunkurin daidaituwar al’amura. Lamarin da ya sa suka ba shi lambar yabo.
Taron da aka yi a makon jiya a nan Yamai a tsakanin Hafsan Hafsoshin Nijar da takwaransa na Najeriya na daga cikin nasarori masu nasaba da ayyukan tuntubar da jakadan Najeriya Mohammed Sani Usman ya gudanar a kokarin farfado da hulda a tsakanin kasarsa da Nijar.
Da yake karbar lambar yabon da aka ba shi jakada Usman ya jaddada girman dangantakar kasashen biyu.
Kungiyoyin sun kuma yi amfani da wannan dama don jan hankulan shugabanin kasashen Nijar da Najeriya dangane da nauyin da ya rataya a wuyansu a matsayinsu na masu rike da lamuran mulkin al’umomin da ke tamkar hanta da jini.
Nijar da Najeriya masu iyakar da ta haura kilomita 1,500 na da alaka a fannoni da dama.
Ko baya ga huldar da ke tsakaninsu a karkashin inuwar CEDEAO/ECOWAS kasashen biyu na tafiyar da harkokin rayuwar al’umominsu a karkashin hukumar hadin gwiwa ta Niger Nigeria Joint Commission haka kuma suke da hadin gwiwa a rundunar kasashen tafkin Chadi ta MNJTF mai yaki da Boko Haram kamar yadda a dai gefe dakarun Najeriyar da Nijar ke hada kai don fatattakar ‘yan bindigar da ke addabar jama’ar garuruwan iyaka.
Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5