Matakin tsige Mohammed Ali Ndume daga mukamin Mai tsawatarwar ya biyo bayan wata wasika ne da ke dauke da sa hannun Shugabanin Jamiyyar APC na kasa Abdullahi Umar Ganduje da Sakataren Jamiyyar Barista Ajibola Bashiru.
Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ne ya karanta wasikar inda ya ce jamiyya ba ta ji dadin bayanan Sanata Ali Ndume da yayi a gidan telebijin din ARISE ba, ganin cewa yana daya daga cikin jigajigan Jamiyyar APC. Akpabio ya ce jamiyya ta nemi Majalisa ta ladabtar da Ndume, kuma ta ba Ndume dama ya fice daga Jamiyyar APC ya koma kowace Jam'iyya.
To sai dai Forfesa Dahiru Mohammed Sani na tsangayar Nazarin aikin lauya a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria ya ce, Majalisa ba ta yi daidai ba wajen tsige Ali Ndume, saboda babu inda doka ta ce a tsige dan Majalisa idan yayi wani laifi a wajen Majalisa. Sani ya ce, kamata yayi jamiyya ta dauki mataki akan Ndume tunda dan Jamiyya ne shi, ko kuma wadanda ya yi wa laifi suna iya shigar da kara akan sa.
Shi kuwa kwararre a fanin siyasa da diflomasiyar kasa da kasa kuma malami a Jami'ar Abuja, Dokta Farouk Bibi Farouk ya yi tsokaci cewa, a tsarin siyasar da ake bi a Najeriya na Shugaba mai cikakken iko, Jamiyya ba ta da hurumin ba bangaren Majalisa umurni, sai dai ta bada shawara. Bibi ya ce Jam'iyu sun huda ne sun ga jini domin sun yi wa Sanata Abdul Ningi amma babu wanda ya kare shi, wannan ya nuna cewa wannan tsari ne na fako, saboda haka yana mai bada shawarar a yi taka tsantsan.
Duk kokarin da Muryar Amurka ta yi na jin ta bakin Sanata Ali Ndume dangane da lamarin ya ci tura.
Sanata Ali Ndume ba ya a Majalisar a lokacin da aka dauki matakin tsige shi.
Saurari cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5