Zauran matasa ya samu bakuncin wasu magidanta, wanda suka tattauna kan dalilan da suke haddasa mutuwar aure a kasar hausa, bakin sun bayyana ra’yoyinsu da suke ganin sune ke mukaddashin samun rabuwar auren musammam a wannan zamani.
Alhaji Sani Ibrahim Ganko dai na ganin dalilai biyu ne ke kawo rabuwar aure kasar hausa, wanda yace na farko dai shine rashin hakuri, na biyu shine rashin sanin ka’idar auren, rashin sanin dalilan aure ga miji da mata kan janyo mutuwar aure baki ‘daya da zarar an ‘daura. Ya cigaba da bayar da missal kan yadda aure yafi mutuwa a wannan zamani fiye da zamanin baya, hakan ya faru ne kasancewar mutanen sun sani kuma sun rike dalilan yin auren, sun kuma zauna da ‘dadi ba ‘dadi.
Shikuma Alhaji Abubakar Tsari na ganin cewa yin auren dole shine makasudin samun rabuwar aure a wannan zamanin, idan aka duba yadda ake yiwa mata wasu lokuta a ‘daura musu aure da wanda basa so, to kuwa duk abinda miji zai kawo mace bazata darajar sa ba, ya kuma cigaba da janyo hankalin iyaye kan idan har za’a yi wa ‘ya mace aure aka fuskanta babu soyayya tsakanin ta da wanda za’a aura mata to a hakura, idan har kuwa a ka yanke hukunci cigaba da auren to abinda ake gudu kan iya faruwa.
Abinda ke kawo tabarbarewar aure a wannan zamani inji Malam Nura, shine rashin fuskantar zamantakewa da wasu mata keyi, kamar yadda mai gida ya saba shigowa da abinda Allah ya hore cikin gida, to idan aka sami canji duniya ta ‘dan juwa Allah bai hore abinda aka saba samu ba, amma wasu matan basa ganewa an shiga wani hali.
Saurari tattaunawar ta zauren matasa.