Wani mutum ‘dan jihar Flolarida ya kai karan asibitin jihar zuwa kotu, a dalilin shiga damuwa da yawan tunani da yake kasancewar asibin ne suka yi masa aiki inda aka yanke masa kafar sa ta dama, bayan da aka yanke ta an kuma jefar da kafar a shara wadda ba’a cire takarda nan mai ‘dauke da sunansa ba wadda ake rubutawa domin a sanin ko ta waye.
Mutumin mai suna John Timiriasieff, mai shekaru 56 da haihuwa anyi masa aikin yanke kafar ne ta dama ne a cikin watan Oktoban shekarar data wuce a wani asibiti mai suna Doctor’s Hospital dake garin Coral Gables dake jihar Florida.
A ranar Larabar data wuce ne mutumin ya kai karan asibitin da yayi masa aikin, inda takardar karan take cewa, “kamar yadda yakamata bayan an yanke kafar a zubar da ita yadda dokar jihar Florida ta tsara, amma asibitin ya jefar da kafar cikin shara, ‘dauke da takarda mai bayyana sunan mai ‘kara.”
Wata ‘daya bayan da aka yanke wa mutumin kafa, ‘yan sanda masu bincike kan mutanen da aka kashe ne suka tuntubi iyalin sa domin sun sami kafar kuma suna tunanin an kashe John.
Daga jin wannan labari ne iyalan mutumin suka ‘dunguma zuwa asibitin domin neman sanin abinda ya faru hark afar ta kai ga shara, wanda asibitin yaki basu wani bayani kan abinda ya faru.
Lauyan mai kara dai yace, mutumin da yake karewa ya shiga cikin damuwa da ‘bacin rai ga asibitin, kuma dole asibitin ya dauki laifin haddasa hakan ga John, asibitin dai ya gaza kare hakkin mutane da bin dokar jiha.