Kimanin shekaru 42 ke nan da Allah ya yi wa Janar Murtala Muhammad rasuwa amma har yanzu ana tunawa da shi sanadiyar abubuwan da ya yi cikin kwanaki 200 da ya yi yana mulki.
A cewar Malam Ibrahim Ado Kurawa, wani masanin tarihi kuma daga jihar Kano - jihar shi marigayin, Janar Murtala mutum ne mai kishin kasa da kaunar jama'arsa da son hadin kan duk 'yan kasar.
Malam Kurawa ya ce Janar Murtala ya lura cewa tsarin mulkin Burtaniya da kasar ta gada a lokacin da aka bata 'yanci shi ne ummul aba'isin rarrabuwar kawunan 'yan Najeriya. A cewarsa, shirin ya tanadi zaben mutum daga garinsu kana ya je tarayya inda yana iya zama shugaban kasa. Wannan shirin ya sa babu shugaban da yake ganin kasar tamkar daya ce sai dai inda ya fito.
Janar Murtala Muhammad shi ya samar da shirin gwamnatin da ake amfani da shi. Haka zalika, shi ya samar da babban birnin tarayya kuma ya dora tubalin samun jam'iyyu da za su nemi tsayawa takara a duk fadin kasar. Shi kuma ya fara aika ma'aikata daga wannan bangaren zuwa wancan ba tare da yin la'akari da inda mutum ya fito ba.
Baya ga wadannan abubuwan, Janar Murtala Muhammad shi ne shugaban Najeriya na farko da ya yi yaki da cin hanci da rashawa gadan-gadan.
Ga Mahmud Ibrahim Kwari da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5