A ranar asabar wadansu mata uku suka kai hare haren kunar bakin wake a garin Gwoza na jihar Borno da su ka yi sanadin mutuwar sama da mutane 30, yayinda kusan dari suka ji raunuka bisa ga cewar jami’ai.
A hirar ta da Muryar Amurka, Helen Bako wata ma’aikaciyar kula da jin dadin jama’a wadda ta shafe kusan shekaru 25 tana aikin kula da mata da kananan yara a jihar California kasar Amurka ta bayyana cewa, yana da wuya uwa ta yi wani abin da zai sa rayuwar ‘ya’yanta cikin hatsari, sabili da haka ganin daya daga cikin matan da su ka kai harin kunar bakin wake na baya bayan nan a jihar Borno manuniya ce cewa, akwai wani babban dalilin da ya sa matan su ka kai harin.
Madam Helen ta ce akwai muhimman dalilai guda uku da za su iya sa mata su sadaukar da rayukansu haka, da suka hada da tsoro, neman karbuwa ga wanda ya nuna masu kauna, da kuma rashin kulawar hukumomi da al’umma.
Bisa ga cewar Madam Helen, idan kungiyoyin ta’addanci ko kuma miyagu su ka kama mata, sukan tsorata su, su ga cewa, basu da wata mafita idan suna so su ceci rayukan danginsu ko iyalansu, ko kuma gujewa wata mawuyaciyar rayuwa da za su shiga idan suka ki kai harin.
Na biyu kuma, matan suna iya mika wuya su sadaukar da rayuwarsu, su amince da kai irin wadannan hare haren idan al’umma ko danginsu su ka yi watsi da su, suka bar su cikin wahala kafin ‘yan ta’adda su dauke su su fara nuna masu kauna da yi masu zakin baki cewa, sun fi dangin da suka baro kaunarsu da kula da rayuwarsu har su rinjaye su. Idan irin wadannan mata su ka ga yadda ‘yan ta’addar su ke kula da su, ko da a baka ne kawai, sai su ga kamar gaskiya ne, saboda haka su kan yarda su yi duk abinda wadannan mutanen su ka sa su, ko da kuwa zai cutar da danginsu.
Na uku kuma bisa ga cewar Madam Helen, wadansu matan suna yarda su kai harin kunar bakin wake ne sabili da alkawarin igancin rayuwa ko kuma wani lada da aka alkawarta masu idan su ka kai harin ko da kuwa zai kai ga rasa ransu. ‘Yan ta’adda su kan rude su cewa, idan sun mutu a harin, za su sami wani lada a gaba. To rashin zurfin fahinta ya kan sa matan gaskanta abinda ‘yan ta’addan su ka gaya masu, su yarda su kai harin.
Wannan dai ba shi ne karon farko da mata suka kai harin kunar bakin wake ba da ya yi sanadin rasa rayuka a Najeriya. A watan Yunin 2014, wata mata mai a kan babur ta je barikin sojoji a Gombe ta tayar da bama-baman da ke daure a jikinta, a wurin da ake binciken ababan hawa, ta kashe kanta lamarin da wani soja. Wannan ne karon farko da aka kungiyar da ke tada kayar baya da kai hare hare a arewa maso gabashin Najeriya, Boko Haram ta fara amfani da mata wajen kai hare hare. Wannan kuma ya sa kungiyar shiga wani rukuni na kungiyoyin ta’addanci.
Duk da yake kawo yanzu, babu kungiyar da ta dauki alhakin kai hare haren kunar bakin waken na ranar asabar, Kingiyar Boko Haram ta yi amfani da mata da kananan yara mata tsakanin shekaru 7 zuwa 17 wajen kai hare haren kunar bakin wake da bincike ya nuna cewa, a cikin shekara daya, kungiyar Boko Haram ta yi amfani da a kalla mata 90 wajen kai hare haren kunar bakin wake da su ka yi sanadin mutuwar a kalla mutane 1,200 da kuma raunata da dama. Lamarin da ya maida Kungiyar Boko Haram. kungiyar ta'addanci da ta fi cin zarafin mata a duniya.
An dauki shekaru da dama tun bayan kashe shugaban kungiyar Abubakar Shekau a shekara ta 2021, ba a yi amfani da mata wajen kai hare haren kunar bakin wake ba, kafin harin da mata uku suka kai ranar asabar na makon jiya.
Masana sun bayyana cewa, ‘yan ta’adda suna amfani da mata wajen kai harin kunar bakin wake ne sabili da yana da wuya a bincike su kasancewa ba za a zaci zasu kai irin wadannan hare haren ba. Banda haka kuma, in ji masana, amfani da mata ko kananan yara wajen kai hare haren kunar bakin wake, alama ce cewa, an sa ‘yan ta’addar a kwana, suna so su nuna har yanzu suna da karfi, ko kuma su nemi dauke hankalin hokumomi daga kansu, ko neman jan hankalin ‘yan jarida.
Ku Duba Wannan Ma Gwamnatocin Najeriya Da Amurka Sun Yi Allah-wadai da Harin Kunar Bakin Wake Da AKa Kai Jihar Borno