Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatocin Najeriya Da Amurka Sun Yi Allah-wadai da Harin Kunar Bakin Wake Da AKa Kai Jihar Borno


Wani kunar bakin wake da aka kai Maiduguri, Yuni 22, 2015.
Wani kunar bakin wake da aka kai Maiduguri, Yuni 22, 2015.

Shugaba Bola Tinubu ya yi Allah-wadai da harin kunar bakin wake da aka kai ranar Asabar a jihar Borno da ya bayyana matsayin ta'addanci, yayinda gwamnatin Amurka ta bayyana niyar hada hannu da gwamnatin Najeriya wajen yaki da ta'addanci.

Shugaba Tinubu ya jajantawa iyalan wadanda harin ya rutsa da su, da kuma gwamnatin jihar Borno a cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Lahadi ta hannun mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale.

Shugaba Tinubu ya bayyana hare-haren a matsayin ta’addanci da ya nuna irin matsin lambar da ‘yan ta’adda ke fuskanta da kuma nasarar da aka samu wajen rage karfinsu na kaddamar da hare-hare."

ADAMAWA: Harin kunar bakin wake a Mubi
ADAMAWA: Harin kunar bakin wake a Mubi

Shugaba Tinubu ya kara da cewa, "masu tayar da hankali zasu gamu da mummunar makoma kuma wadannan hare-haren matsorata ne kawai da ba zasu iya maida hannun agogo a baya ba, saboda gwamnatinsa ba za ta bar al’umma ta koma zamanin fargaba da hawaye, da bakin ciki, da zubar da jini ba.”

Ya kuma bada tabbacin cewa, gwamnatinsa na daukar matakan da suka dace domin tabbatar da tsaron ‘yan kasa, tare da jaddada cewa, za a kara zage damtse wajen ganin an kawar da wadanda ke addabar al’umma da katse wa mutane hanzari.

Wani harin kunar bakin wake a Maiduguri
Wani harin kunar bakin wake a Maiduguri

A halin da ake ciki kuma, gwamnatin Amurka ta yi Allah wadai da harin da ta bayyana a matsayin rashin Imani.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya Lahadi, gwamnatin Amurkan ta hannun ofishinta a Najeriya, ta jaddada aniyar ta na hada kai da gwamnatin Najeriya domin murkushe ayyukan ta'addanci da kuma hukunta miyagu.

Sanarwar ta kara da cewa, “Amurka ta yi Allah wadai da munanan hare-haren da aka kai a Gwoza, jihar Borno a ranar 29 ga watan Yuni. Muna mika ta’aziyyarmu ga iyalai da abokan wadanda aka kashe, tare da yi wa wadanda suka jikkata fatan samun cikakkiyar lafiya. Wannan munanan hare-haren manuniya ce ta irin barazanar da ta'addanci ke yi a yankin.

Harin Kunar Bakin Wake Kusa da Garejin Muna a Maiduguri
Harin Kunar Bakin Wake Kusa da Garejin Muna a Maiduguri

Akalla mutane 18 ne suka mutu a ranar Asabar, sannan wasu da dama suka jikkata sakamakon hare-haren kunar bakin wake da aka kai a garin Gwoza na jihar Borno

Hukumomi a jihar Borno sun bayyana jiya lahadi cewa, wadansu mata uku ‘yan kunar bakin wake sun kai hari a wajen wani bikin aure, da wurin jana’iza, da kuma asibiti suka kashe akalla mutane 18.

Kawo yanzu, babu kungiyar da ta dauki alhakin hare-haren.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG