“Daliban Kagara na nan a yankin Birnin Gwari da ke jihar Kaduna, kuma ina da yakini nan ba da jimawa ba, za su koma gidajensu.” Matawalle ya fadawa shirin “Sunday Politics” na gidan talbijin din Channels.
Kalaman gwamman na zuwa ne sa’o’i bayan da aka kubutar da fasinjan motocin sufurin bas NSTA da ke jihar, wadanda wasu ‘yan bindiga suka yi awon gaba da su a ranar Lahadin.
Sakatariyar yada labaran Gwamnan jihar Nejan Madan Mery Barje ta ce Gwamnati na nan tana iya kokarinta wajen ganin ta kubutar da ‘yan makarantar.
Sannan ta ce babu kudin fansa da suka biya kafin kubutar da fasinjan bas din.
Gwamnan Jihar Neja Abubakar Sani Bello, ya ce yanzu sun dukufa ne wajen ganin an kubutar da daliban kwalejin Kagara da ‘yan bindiga suka sace a farkon nan.
Wani sakon Twitter da aka wallafa a shafin Twitter na gwamnatin jihar ta Neja ne ya bayyana hakan yayin da hukumomi ke sanar da nasarar kubutar da fasinjojin motocin sufurin jihar da aka sace gabanin kwashe ‘yan makarantar na Kagara.
“Gwamnati na kara kaimi wajen ganin an saki dalibai, malamai da iyalansu da ke kwalejin kimiyya ta Kagara.” Sanarwar ta ce.
A halin da ake ciki kuma wasu ‘yan bindigan sun kai wani sabon hari a kauyen Gurmana da ke yankin karamar Hukumar Shiroro ta jihar Nejan inda sukayi awon gaba da matan aure da yara sannan wasu yaran kimani 10 da suka firgita sun fada ruwan kogin Gurmanan a cewar wani mazaunin garin Malam Bala Gurmana.
Ko da yake rundunar ‘yan sandan jihar Nejan ba ta ce komai ba akan wannan lamari ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, amma Sakataren Gwamnatin jihar Nejan Alhaji Ahmed Ibrahim Matane ya tabbatar da aukuwar lamarin.
Shi ma shugaban hukumar ba da agajin gaggawa a jihar Nejan Alhaji Ibrahim Inga ya ce duk da yake aikin ceton yana da hadarin gaske amma suna iya kokarin ganin an ceto yaran.
Wannan hari na Gurmanan dai yana zuwa ne a dai dai lokacin da Gwamnatin jihar Nejan ke ci gaba da tattaunawa da ‘yan bindigan da nufin yin sulhu.
A saurari rahoto cikin sauti daga Mustapha Nasiru Batsari:
Your browser doesn’t support HTML5