Makarantu sun kasance a rufe a sakamakon nuna juyayi akan rasuwar dalibi Mala Bagale wanda ya hadu da ajalinsa a farfajiyar jami'ar Yamai a bara. Yayin da shugabannin kungiyar dalibai ta USN suka hallara a gaban kotun Yamai domin jin halin da ake ciki game da karar da suka shigar a watan Satumban 2017, a kokarinsu na neman adalci, saidai da alama ana gidan jiya inji Muhammad Iddar, sakataren kungiyar dalibai ta kasar wato USN.
A washe garin mutuwar dalibin Mala Bagali, iyayen mamacin sun ziyarci fadar shugaban kasa wanda ya jajanta musu akan wannan rashi abinda Mallan Muhammadu, wani mashawarci a fadar shugaban kasar Nijar yake cewa alama ce dake nuna kyakyawar aniyar gwamnatin kasar wajen neman haske akan abinda ya wakana, inda yace sun tattauna da shi an kuma kafa kwamiti don su gano wanda ya aikata. Ya kara da cewa akwai jami'an tsaro da yawa a lokacin baza a iya gano ko wa ne ne ba.
Wasu bayanai da aka bayar jim kadan bayan ganawar su da shugaban kasa na cewa sun rungumi kaddara, saidai jami'an fafutuka irin su Salisu Amadu na cewa maganar Mala Bagale wani abu ne da ya shafi 'yan kasar Nijar baki daya, ya ce ko da iyaye sun yafe ba zai yiwu ba dole a dubi lamarin.
A rahoton da ya bayar a watan Agustan da ya gabata, wani kwamitin bincike da aka kafa a karkashin hukumar kare hakkin dan adam ta CNDH, wanda kuma ya kunshi bangarori da dama ya tabbatar da cewa harbin ya daki wannan dalibi a goshinsa a maimakon buga kanshi da dutse da hukumomin Nijar suka bayyana a washegari.