A shekaran jiya litinin dai an tashi baran-baran a zauren tattaunawa tsakanin wakilan kungiyar ta ASUU da na gwamnati, sai dai masana harkokin ilimi a Najeriya na ra'ayin cewa, shugabannin hukumomin ilimi ba sa taka rawar data kamata wajen warware wannan takaddama.
Hakan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da kwararru dake bin diddigin alkaluma a fannin ilimi ke cewa, fiye da dalibai miliyan 13 ne suka nemi gurabe a Jami'o'in Najeriya cikin kasa da shekaru 7 da suka shude.
Wadansu dalibai da Sashen hausa ya yi hira da su sun bayyana damuwa ganin nan ba da dadewa ba za a komawa makaranta, suka kuma ce babu shakka zai shafi karatunsu idan har aka kai lokacin ba a janye wannan yajin aikin ba.
Wani dalibi ya bayyana cewa, yana cikin rubuta jarabawa aka sanar da yajin aikin, kuma nan take malaman jami’ar suka dakatar da duk wani abinda ya shafi harkokin ilimantawa da ya hada da sa ido kan rubutun ayyukan binciken kamala jami’a.
Saurari cikakken rahoton
Your browser doesn’t support HTML5