Yayin da kungiyar malaman jami'a ke cigaba da yajin aiki daliban kasar sun goyi bayan malamansu wadanda suka ce fafitikar da su keyi ta kare rayuwar su daliban ne.
WASHINGTON, DC —
Daliban Najeriya sun ce dalilinsu ne malamansu suka sa wando kafa daya da gwamnatin tarayya domin su kare rayuwarsu su kuma ingantata.
Wani mai magana da yawun daliban a taron gangami da suka shirya ya ce malaman sun yi yarjejeniya da gwamnati wanda dukansu suka sama hannu. Don haka wajibi ne gwamnati ta aiwatar da yarjejeniyar ba tare da wani kumbiya-kumbiya ba. Ya ce gaskiyar ita ce kungiyar malaman wato ASUU tana tanada masu rayuwarsu ne sabili da haka suna bayan malaman dari bisa dari. Gwamnati ta biya bukatar ASUU. Ta gyara masu wuraren kwana da samarda kayan aiki da dai sauransu.
Wani matashi Isa Musa Yaro ya ce kodayake hakin gwamnati ne ta samar ma matasa aikin yi yakamata su ma matasan su zama masu kishin zuci ta yadda zasu taimakawa kansu da kansu. Ya ce ba daidai ba ne kowane matashi ya nemi gwamnati ta bashi aiki. Abun da yakamata gwamnati ta yi shi ne ta kirkiro ma'aikatar koyan sana'o'i inda kowane matashi dole sai ya koyi wata sana'a. Idan matashi yana da aikin yi a gabansa ba zai bi dan siyasa ba ko ya nemi tada fitina. Ya ce 'yan siyasa basu damu da rayuwar matasa ba illa dai su basu shaye-shaye da makamai domin su razana wadanda suke hamaya da su. 'Yan siyasa babu abun da suke koyawa matasa sai zage-zage da fada. Kamata ya yi matasa su tashi tsaye su rike amana su kuma aikata adalci.
Hayiya Mariya Awalu shugabar kungiyar dake fafitikar neman zaman lafiya tsakanin addinai daban daban ta ce mata suke shiga matsala a duk lokacin da aka yi tashin hankali don haka suke kokarin tallafi masu. Idan an yi tashin hankali mata ne da 'ya'ya ke shan wahala. Su ne zasu ta yin fama da neman abun da 'ya'yansu zasu ci. Idan yaro ya gama makaranta kuma babu aikin yi to shi ke nan idan ya gaji da zaman banza sai ya kama shaye-shaye da yin fada da mutane.
Shi ma Manjo Hamza Al-Mustapha da ya halarci taron ya bayyana cewa matasa a Najeriya na cikin halin kakanikayi. Suna fama da rashin makaranta da rashin tsaro ga kuma shaye-shaye. Suna fama da rashin samun alkibla da rashin samun sana'ar yi da aiki. Ya ce wasu maganganunsu tamkar sabo ne domin sun gaji da duniyar ma. Ya kamata a hada kansu. A bullo da hikimomi yadda zasu samu aikin yi su kare martabarsu a matsayinsu na kasancewa matasa na gari a kasar.
Zainab Babaji nada rahoto.

Your browser doesn’t support HTML5