Ana ci gaba da yin Allah wadai da rikicin Burma da ya ki ci ya ki cinyewa, inda rahotannin ke zargin cewa ana aikata kisan kare dangi akan tsurarun Musulmi 'yan kabilar Rohingya.
WASHINGTON D.C. —
Shugaban mabiya addinin Buddha na Tibet, Dali Lama ya yi kira ga jagorar kasar Myanmar, Aung San Suu Kyi da ta kokar ta ta ga cewa an kawo karshen tashin hankalin da ke addabar ‘yan jinsin Rohingya na kasarta.
A cikin wasikar da ya rubuta mata, shugaban addinin na mutanen Tibet ya ce yana mamakin yadda lamarin ke kara sukurkucewa kusan a koda yaushe.
Haka kuma Dalai Lama ya gargade shugabar ta Myanmar da sauran shugabannin kasar cewa muddin ba su shawo kan wannan matsalar ba to ba shakka hakan zai iya janyo karuwar tashin hankali da nakasar kadarorin jama’a a cikin kasar.