Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Gwagwarmayar Rohingya Sun Nemi a Tsagaita Wuta


'Yan gudun hijrar kabilar Rohingya a lokacin da suke karbar tallafin abinci a Bangladesh, ranar 9 ga watan Satumba 2017.
'Yan gudun hijrar kabilar Rohingya a lokacin da suke karbar tallafin abinci a Bangladesh, ranar 9 ga watan Satumba 2017.

Masu gwagwarmayar 'yan kabilar Rohingya sun nemi a tsagaita wuta a rikicin da ake fama da shi a jihar Rakhine dake kasar Myanmar.

Rahotanni daga Myanmar suna cewa, masu fafutika ‘yan kabilar Rohingya, sun yi kiran a tsagaita wuta na tsawon wata guda, domin masu ayyukan ba da agaji su sami damar kaiwa ga wadanda rikici ya rutsa da su.

Masu gwagwarmayan wadanda suke kiran kansu “Arakan Rohingya Salvation Army ko kuma ARSA a takaice, sun kai hare-hare a wasu ofisoshin ‘yan sanda da wani barikin soji a watan da ya gabata, lamarin da ya jirkice ya kai ga tilastawa sama da mutane dubu-dari uku ficewa daga muhallansu.

A wata sanarwa da suka fitar a jiya Asabar, kungiyar ta yi kira ga masu ba agajin gaggawa da su koma kai dauki ga wadanda rikicin ya shafa, ba tare da sun yi la’akkari da kabila ko kuma addinin mutum ba, yayin wannan tsagaita wutar.

Wannan kira na neman a jingine fadan, na zuwa ne kwanaki kadan bayan da Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin, Nikki Haley, ta tunatar da hukumomin Myanmar cewa, duk da Amurka na goyon bayan yaki da masu ta da tarzoma a arewa maso yammacin jihar Rakhine, dole ne a ba da kofar kaiwa ga wadanda rikicin ya shafa domin a agaza musu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG