WASHINGTON, DC —
Gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike, ya yiwa ‘yan wasan Super Eagles alkawarin Dala Amurka 20,000 a duk kwallon da suka zura a raga a wasansu da kasar Swaziland, da za’a buga yau din nan a Garin Port Harcourt.
A wasan da suka buga a zagayen farko a kasar Swaziland, Super Eagles sun raka sun sami yin kunnen doki amma Sunday Oliseh nada kwarin gwiwar cewa ‘yan wasan Super Eagles, zasu yi nasara.
A yau ne za’a buga wasan a filin wasa na Adokie Amesiemaka,
Sakataren Gwamnatin jihar Rivers Kenneth Kobani, wanda ya isar da sakon Gwamnan na bada dala 20,000, a duk kwallon da suka zura a ragar ‘yan Swaziland, ya bukaci ‘yan wasan da suyi duk abunda ya dace domin samun nasara.