Tun a ‘yan kwanakin bayane wasu masana ke ta nuna damuwar su, dangane da irin canji da ake samu a fadin duniya. Tun bayan irin cigaba da ake samu wajen kera mutun-mutumi wato “Robot” domin kuwa suna gani cewar bada dadewa ba za’a kai wani matsayi da robot zasu dauke abubun da mutane kanyi da dama.
A cewar “Bank of Enfland” kimanin nan da wasu shekaru kadan masu zuwa a kasar Amurka kadai, mutun-mutumi robot zasu dauke ayyukan sama da mutane milliyan tamanin 80M, haka ma a sauran sassa na duniya za’a fuskanci matsalar rashin aikin yi.
Kamfanin Google, sun fitar da mutun-mutumin su “Robot” a karon farko da aka kai shi cikin wani daji, don ganin yadda zai gudanar da mu’amar shi, da kuma yadda idan aka saka shi cikin jama’a, ta ya zai yi rayuwar shi. Suna ganin cewar akwai ire-iren ayyuka da dama da robot zai iyayi cikin gaggawa batare da ansa mutun yayi ba. Domin kuwa wadannan robot din da ake kirkira, suna da kwakwalwa da ake sa musu, zasu yi tunani na yadda abu yakamata ayi shi a kuma lokacin da yakamata. A takaice za'a ce suna abubuwa kamar mutane.