Dakota Ta Ware Wa Ilimi Makudan Kudade

Wata makaranta da dalibai

‘Yan majalisun dokokin Jihar Dakota da ke kasar Amurka sun amince da Karin dala miliyan shida a cikin kudin kasafin bana domin a inganta ilimi a jihar.

Wadannan kudade za a yi amfani da su ne a matakin farko na zangon karantun shekarar 2015 zuwa na 2016.

Rahotannin sun ce, karin kudaden an yi su ne da manufar kara tallafawa dalibai ‘yan kasa da basu da karfi.

A cewar shugaban kwamitin da ke lura da ilimi a majalisar dokokin kasar, kimanin yara miliyan shida ‘yan kasa da shekaru biyar ne za su ci gajiyar wannan shiri, inda za a kashewa kowane yaro kimanin dalar Amurka 1,500.