Sana’ar hannu itace mafita a harkar yau da kullun, ita sana’ar hannu bata tsufa balle ace mutun yarasa aikin yi. A tabakin Nasiru Isah Abdullahi Alkali, shi sana’r shi dinkin kaya kuma ya kwashe shekaru ashirin da biyu yana wannan kasuwancin, amma saboda halin yau da kullun yasa abubuwan rayuwa sun juya mishi.
A wannan sana’ar yasamu ya kamala karatun shi na sakandire kuma yana da iyalai wanda yake dauke da nauyin su duk ta sana’ar shi ta dinki, wanda daga bisani yasamu wasu matsalolin a rayuwa wanda ya kai shi da siyar da kayan aikin shi ya koma kasan wata mata yana mata aiki tana biyanshi a duk wata.
Ganin cewar yana da hazakar da basirar shiyasa aka dauke shi yayi wannan aiki wanda idan da baida wannan ilimin na sana’ar to da zai koma bashi da abun da zai taimaka ma iyalansa bale kansa. Don haka yayi kira ga matasa ‘yan uwanshi dasu tashi tsaye wajen samun sana’ar hannu da zasu iya dogaro da ita don koda sun samu jarabawar rayuwa zasu iya tashi batare da wata damuwa ba.
Kuma matasa su sani cewar ta ko ina sune manyan gobe don haka yakamata su zaba ma kansu hanyar rayuwa mai inganci kuma wanda zai taimaki al’umah da cigaban kasa baki daya, kasancewar ba gwamnati kadaice zata dinga daukar dawainiyar al’uma ba kawai, suma sai sun bata dasu gudunwa don cigaban kasa.