Dakatar Da Sanusi Lamido Sanusi Na Iya Shafar Tattalin Arziki

Sanusi Lamido Sanusi.

Masanin tattalin arziki, Yusha'u Aliyu, yace takardar kudin Naira zata ji jiki na gajeren lokaci, yayin da masu jari zasu fara janyewa don rashin tabbas
Wani masanin tattalin arziki yayi hasashen cewa tattalin arzikin Najeriya zai samu illa na wani dan lokaci a sanadin dakatar da gwamnan babban bankin Najeriya, Sanusi Lamido Sanusi, har zuwa lokacin da za a samu tabbas a kan alkiblar duk wadanda za adora kan jagorancin bankin.

Yusha'u Aliyu yace masu bayarda basussuka na kasashen waje zasu yi dari-darin bayarwa da kasar wani sabon bashi a wannan lokaci, abinda zai takura kasafin kudi.

Haka kuma, takardar kudin Najeriya, Naira, zata fadi idan an kwatanta da kudaden musanya a yayin da kamfanonin kasashen waje zasu sayar da kudaden da suke rike da su a Naira su fitar da kudaden zuwa wuraren da suka fi tabbas.

Ita ma kanta, ministar kudi, kuma mai kula da tattalin arzikin Najeriya, Ngozi Okonjo-Iweala, ta furta cewa lallai dakatar da Sanusi Lamido Sanusi, zata shafi tattalin arziki da kuma kudin Najeriya na gajeren lokaci, amma ta tabbatarwa da masu zuba jari cewa gwamnati zata ci gaba da aiwatar da manufofinta na tattalin arziki, babu abinda zai canja.

Ga cikakken bayani daga bakin masanin.

Your browser doesn’t support HTML5

Yusha'u Aliyu, Kwararre Kan Tattalin Arziki Ya Fasa Bakin Dakatar Da Sunusi Lamido Sunusi - 6'40"