Dakarun Tsaron Pakistan Na Daukar Matakan Dakile Yan Ta'adda

Rundunar sojin kasar Pakistan tace wani sabon harin da aka kai ta sama kusa da kan iyaka da Afghanistan ya kashe a kalla mayaka goma sha hudu ya kuma jikkata sha daya.

An lalata maboyar mayakan tara a harin da aka kai ta sama da kuma kasa a kwazazzabon kabilu na Khyber, bisa ga cewar kakakin rundunar soji Laftanar janar Asim Bajwa jiya talata.

Khyber na daya daga cikin yankunan kabilu bakwai a Pakistan dake da dan ikon cin gashin kai, wanda yake kan iyakar Afghanistan. Yankin maboyar mayaka da masu aikata miyagun laifuka ne da jimawa, wadanda ake dorawa alhakin hare haren ta’addanci da ake kaiwa kasashen biyu.

Sai dai hukumomin kasar Pakistan sun ce, yunkurin kakkabe ayyukan ta’addancin da ake yi a cikin shekarun nan ya gurguntar da su a yankin, yayinda dakaru suka maida hankali kan samar da tsaro a kan iyakar mai fadin kilomita dubu biyu da dari shida.

Dakarun tsaron kasar Pakistan sun kara daukar matakan dakile ayyukan ta’addanci da suka hada da ayyukan leken asiri a kewayen kasar, biyo bayan harin kunar bakin waken da aka kai ranar takwas ga watan Agusta a wani asibiti dake birnin Qyetta kudu maso gabashin kasar. Harin ya kashe mutane saba’in da hudu ya kuma raunata da dama.

Kungiyar Taliban ta kasar Pakistan da ake kira Jama’at-ul Ahrar ta dauki alhakin harin.