Rundunar ta Rasha ta dade tana irin wa’yannan hare hare da nufin taimakawa gwamnatin Syria ta shugaba Bashar Al-Assad tun Satumban bara. Wannan Talata ce karo na farko da jiragen Rasaha suka fadada haren haren nasu zuwa wata kasar waje, inda mayakan Rashan suka yi amfani da abokiyar Syriar, Iran suna aikawa da bama-bamai a zango mai nesa.
Ma’aikatar tsaron Rasha tace tana wa’yannan hare-haren ne da zummar murkushe kungiyar ISIS da kuma mayakan da wasu kungiyoyin ta’adda dake birnin Aleppo kamar al_Nusrah da sauransu
Wata kafar yada labarai ta gwamnatin Iran , ta ruwaito jawabin shugaban majalisar tsaron kasar, Ali Shamkhani yana cewa Iran da Rasha suna aiki tare don yaki da ta’addanci a Syria kuma suna baiwa juna daman amfani da kasashensu wurin aiwatar da ayyukansu.