Dakarun Syria Sun Kwato Kauyuka, Garuruwa a Hannun 'Yan tawaye

Wasu dakarun Syria yayin wata fafatawa da ake yi a yakin basasar kasar

A karon farko tun bayan da suka kaddamar da hare-hare a gabashin Ghouta a watan da ya gabata, dakarun sun kwato garuruwa da kauyuka shida a hannun mayakan 'yan tawaye.

Kafar yada labarai mallakar gwamnamtin Syria, da kungiyoyin kare hakkin bil Adama, sun ce dakarun gwamnati da gamayyar mayakan sa-kai, sun kwace wasu kauyuka da garuruwa da ke hannun ‘yan tawaye a gabashin Ghouta da ke kusa da Damascus, babban Birnin kasar.

Wannan nasara ita ce mafi girma da suka samu, tun bayan da dakarun na gwamnati suka kaddamar da kai hare-hare a watan da ya gabata.

Kafar yada labaran sojoji ta Syria, ta ce dakarunta sun karbe ikon akalla kauyuka da garuruwa shida da ke gefen gabashin yankin.

A yau Lahadi, kungiyoyin ‘yan tawaye su ma suka kaddamar da hare-haren martani, inda har suka ketara iyakar da dakarun gwamnati suka shata.

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Syrian Observatory for Human Rights, ta ce, akalla gari guda ne ya sake fadawa hannun ‘yan tawayen yayin da ake ci gaba da fafatawa.

Kutsawar da dakarun gwamnati suka yi zuwa cikin gabashin Ghouta, ya sa mutane da dama sun tsere, inda suka rika neman mafaka a yankunan da ke tsakiyar gabashin garin na Ghouta, a cewar gidan talbijin din Orient TV da ke goyon bayan ‘yan tawayen na Syria.