Kungiyar nan mai sa ido kan hakkokin bil adama ta Syrian Observatory for Human Rights da ke da cibiya a Burtaniya, ta ce, dakarun Syria sun isa kan iyakar gundumar ta Raqqa, tare da taimakon hare-haren sama da dakarun Rasha ke kaiwa.
A cewar kungiyar, dakarun na Syria sun yi wata arangama da mayakan IS akan babbar hanyar da ta hada Raqqa da Gundumar Hama da ke kudu maso yammacin kasar.
Dakarun na Syria na sa ran za su dangana da Tafkin Assad da babbar hanyar da ta hada Raqqa da Aleppo, wadda itama wata tunga ce ga mayakan na IS.
Mayakan na IS dai sun rike birnin na Raqqa tun daga shekara 2013, bayan da ta kwace shi daga hanun ‘yan tawaye da ke yaki da shugaba Bashar al- Assad.
Kafofin yada labarai mallakar gwamnatin Syria sun ruwaito cewa an kashe mayakan IS da dama a arangamar da aka yi, sai dai dakarun kasar ba su fitar da adadin mayakan da aka kashe ba.