Sojin Turkiyya Sun Ce Sun Shirya Tsaf Don Kai Wa Siriya Hari

Manyan jami’an sojin kasar Turkiyya, sun ce dakarunsu sun shirya tsaf domin kai wani farmaki cikin Syria da aka jima ana shirya shi, da zimmar kawar da mayakan Kurdawa, wadanda Turkiyyan ta ayyana a matsayin ‘yan ta’adda, amma kasashen yammaci suke kallonsu a matsayin abokai na kut-da-kut a yakin da ake yi da mayakan kungiyar ‘yan ta’adda na IS.

A daren jiya Talata rundunar sojin Turkiyya ta wallafa a shafin Twitter cewa, “dakarunmu da muke tunkaho da su, sun shiryawa wannan farmaki da aka wa lakabi da “Operation Safe Zone.”

Tuni dai wannan sanarwa ta sa jami’an hukumar kai daukan gaggawa na Majalisar Dinkin Duniya, suka kira wani taron gaggawa, Panos Moumtzis, shi ne shugaban tsare-tsaren hukumar a yankin, da maname labarai suka tambaye shi komai zai biyo baya, sai ya ce: Dakarun na Turkiyya dai sun ce ba wai mayakan Kurdawa kawai za su kai wa hari ba, har ma da mayakan IS da ke yankin.