Dakarun Rasha Kusan 100 Sun Halaka a Hadarin Jirgi

Wajen da wani jirgin Rasha ya fadi a sheekarar 2015

Ma’aikatar tsaron Rasha ta ce wani jirgi dauke da sojojin kasar su 92, ciki har da shahararrun mawakan bege, ya fada a Tekun Bahrul Aswad, wato Black Sea, jim kadan bayan ya tashi a wajen wani shakatawa da ke garin Sochi

Hukumomin kasar sun ce an samu baraguzan jirgin da kuma sassan jikin mutane a gabar tekun kasar ta Rasha.

Sannan an samu ainihin gangar jikin jirgin kilomita 1.5 daga gabar tekun, amma nutse a zurfin ruwa da ya kai takin 70.

Jirgin kirar Tu-154 ya bace ne daga kan na’urar da ke bibiyan tafiyar jirage, mintina kadan bayan da ya tashi daga garin na Sochi da misalin karfe 5:40 na safe agogo yankin.

Ya na kuma kan hanyarsa ne ta zuwa wani sansanin soji da ke kasar Syria, inda Rashan ta ke taimakawa dakarun gwamnatin Bashar al Assad yaki da 'yan tawaye.

Ya zuwa yanzu babu karin bayani kan abin da ya haifar da hadarin, kuma hukumomin sun ce zai yi wuya a samu wanda ya tsira da ransa daga cikin mutane kusan 100 da ke cikin jirgin.