Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Ce China Ta Rike Jirgin Amurka Da Ta Kama


Shugaban Amurka mai jiran-gado, Donald Trump a lokacin gangaminsa na karshe a jihar Alabama inda ya je nuna godiya
Shugaban Amurka mai jiran-gado, Donald Trump a lokacin gangaminsa na karshe a jihar Alabama inda ya je nuna godiya

Shugaban Amurka Mai Jiran-gado, Donald Trump, ya ce Amurka ba ta bukatar jirgin ruwanta mara matuki da China ta kama, saboda haka ta rike.

Trump ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter bayan da bayanai su ka nuna cewa Chinan na shirin dawo wa da Amurka jirginta da ta kama a ranar Alhamis.

Ma'aikatar tsaron Amurka ta ce an yi sulhu kan takkadamar, saura yadda za a dawo da jirgin.

Sai dai Chinan ta zargi Amurka da ruruta wutar lamarin, ta na mai cewa za ta maido da jirgin ta hanyar da ta fi da cewa.

A jiya Asabar Trump, ya kammala rangadin da ya ke yi na nuna godiya na zaben sa da aka yi a watan Nuwamba.

Shugaban ya yada zango na karshe ne a jihar Alabama, inda ya gudanar da gangamin yakin neman zabensa mafi girma gabanin zaben.

“Wannan shi ne zai kasance gangaminmu da kuma zangonmu na karshe, ina so na mika godiya ta ga jama’ar Jihar Alabama" In ji Trump.

A lokacin wannan gangami, Sanata Jeff Sessions na jihar ta Alabama ya rufawa Trump baya, shi ne kuma Trump din ya zaba a matsayin wanda zai rike mukamin Attorney Janar.

XS
SM
MD
LG