Ma’aikatar tsaron kasar ce ta bayyana arangamar a wata sanarwa da ta fitar, wacce ta bayyana cewa an kashe ‘yan kungiyar ta Boko Haram su goma, kana an kwace makamai da dama.
Sai dai sanarwar ta ce mayakan sun jiwa wasu sojojin kasar rauni kana an lalata wata motarsu yayin arangamar.
Mayakan sun kai harin ne da misalin karfe shida na yammacin juma'a ne aka kai harin.
Jamhuriyar Nijar ma tana fama da matsalar Boko Haram, musamman tsakanin shekara daya da rabi da ta gabata, inda sukan shiga ta yankin Diffa domin kai hare-hare.
Kasar ta Nijar na daya daga cikin kasashe da ke yankin tafkin Chadi da su ke da dakarun hadin gwiwa a rundunar tsaro da kasashen yankin suka kafa.
Domin jin cikakken bayani saurari rahoton wakilin Muryar Amurka Sule Mumuni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5