Rundunar “Operation Hadin Kai” da ke arewa maso gabashin Najeriya, ta ce ta yi nasarar cafke wani babban mamba a kungiyar Boko Haram.
Wata sanarwar da Kakakin sojojin Birgediya-Janar Onyeama Nwachukwu ya fitar ta ce, Yawi Modu ya shiga hannu.
An jima ana neman Modu ruwa a jallo, saboda irin rawar da yake takawa wajen shirya ayyukan ta’addanci a cewar sojojin Najeriya.
“Bayan da muka samu bayanan sirri, mun samu nasarar cafke Yawi Modu, mamba a kungiyar Boko Haram/ISWAP, wanda dama yana cikin jerin sunayen mutanen da ake nema.” Sanarwar ta ce.
Sojojin Najeriyar sun ce sun kama Modu ne a hanyar Dambo-Wajiroko.
Dakarun na Najeriya sun kuma ce sun yi nasarar kwato wasu kayayyakin da ake amfani da su wajen hada bam din gida a Damboa da ke jihar Borno da kuma Gashua a jihar Yobe.
Kazalika, rundunar ta kuma ce ta yi nasarar gano wani wuri da ake sayar da takin Urea inda daga nan ‘yan ta’adda ke samun kayayyakin hada bama-bamai.
Idan za a iya tunawa gwamnati ta hana sayar da takin na Urea saboda amfani da ake yi da shi wajen hada sinadarin bam.
A ‘yan makonnin nan, dakarun na Najeriya na ba da rahoton cewa mayakan Boko Haram na ta mika wuya saboda nasara da suka ga ana yi akansu.