Dakarun Libya Suna Ci Gaba Da Kai Farmaki Kan 'Yan Tawaye

Wani depon mai yake cin wuta bayan an jkai masa hari a fafatawa tsakanin dakaru dake biyayya ga Gadhafi, da kuma 'yan tawaye a gabshin kasar.

Sojojin dake biyaya ga shugaba Moammar Gaddafi na Libya sun kai hari birnin Ras Lanuf dake hannun yan tawaye kuma suka yiwa mayaka dake ki jinin gwamnati luguden wuta a gabashin kasar suka yi wa masanantar makamashin kasar barna sosai.

Sojojin dake biyayya ga shugaba Moammar Gaddafi na Libya sun kai hari birnin Ras Lanuf dake hannun yan tawaye kuma suka yiwa mayaka dake kin jinin gwamnati luguden wuta a gabashin kasar suka yi wa masanantar makamashin kasar barna sosai.

A jiya Laraba sojojin gwamnati suka kai hari matatar mai dake birnin Ras Lanuf dake hannun yan tawaye. ‘Yan tawaye sunce sojojin Gaddafi sun kai hari akan bututun man daya doshi birnin Sidra kimamin kilomita dari da hamsin gabas da Tripoli baban birnin kasar.

A yammacin kasar kuma gidan talibijin na kasar ya bada labarin cewa sojojin gwamnati ne ke iko da birnin Zawiya inda yan tawaye suka yi kwanaki suna turjewa kawanya ko kuma kokarin kwace birnin da sojojin Libya suka yi. Yan tawayen Libya sunce sun sake kwace tsakiyar birnin.

Babu dai wata kafa ta fisibillahi data tabbatar da wannan ikirari da suka sabawa juna da yake gwamnatin Libya ta hana 'yan jarida shiga Zawiya.

A halin da ake ciki kuma wasu kasashen duniya da kungiyar kawancen tsaro ta NATO suna ci gaba da yin muhawarar akan irin matakin da za’a dauka domin tinkarar rikicin Libya.

Shugaban kungiyar NATO Anders Fogh Rasmussen yace batun Libya da yankin ne zai kasance akan gaba a ajandar taron ministocin tsaron kungiyar da zasu yi a Brussels kasar Belgium a ranar Talata idan Allah ya kaimu.

Sa’anan kuma Ingila da Faransa suna tsara wani kuduri da zai tanadi haramta shawagin jiragen sama a sararin samaniyar Libya.

Shi dai shugaba Gaddafi yayi kashedin cewa kada a kuskura a kaddamar da wannan kuduri.