Ministocin na kasashen larabawa, na ganin saka takunkumin ne kadai zai rage karfin Gaddafi tare da matsa masa lamba kan ya amince a kawo karshen rikicin da Gwamnatinsa keyi da’yan tawaye.Anji manyan jami’an kungiyar kasashen larabawa na cewa an hana jami’an jakadancin Gwamnatin Libya shiga wajen wannan taro na ran Asabar. Ran Juma’a shugaba Barack Obama na Amurka yayi gargadin cewa komai na iya faruwa kan ladabtar da Gaddafi, Amurka na iya maida martani domin hana Gaddafi samun nasarar muzgunawar da yake yiwa masu adawa da Gwamnatinsa.
Taron Shugabannin Kungiyar Kasashen Larabawa Sun Amince Azawa Libya Takunkumin Hana Zirga-Zirgar Jiragen Samanta
Ministocin harkokin wajen kasashen larabawa sun tatauna tattauna ran Asabar a birnin Alkahirar Misra inda suka nazarci tare da kada kuri’ar amincewa azawa kasar Libya takunkumin hana jiragen saman Libya zirga-zirga a wani bangaren sararin samaniyar kasar.