Dakarun Kawancen Yankin Tafkin Chadi Sun Yunkura Wajen Kakakabe Gyauron 'Yan Ta'adda

Kwamandojin rundunar hadin guiwa a Tafkin Chadi.

Sojojin dakarun kawancen yankin tafkin chadi, sun kaddamar da wani aikin kawo karshen burbushin 'yan ta'addan Boko Haram da ISWAP a tsibiran dake zirin yankin tafkin.

Dakarun na Rundunar kawancen kasashen yankin tafkin chadin tare da hadin gwuiwar rundunar OPERATION HADIN KAI, sun fara aikin kakkabe burbushin 'yan ta'addan Boko Haram da ISWAP tun daga Monguno ta bangaren Najeriya zuwa cikin kasar Chadi.

Wata sanarwa da kakakin rundunar ta MNJTF Kanar Kamaruddeen Ademola Adegoke ya aikewa sashin Hausa na Muryar Amurka na cewa, wannan farmaki dai wanda sojojin Najeriya da chadin suka kaddamar tare kuma lokaci guda, an faro aikin ne daga sansanoni da dama da su ka hada da Grada, kwatan mai shayi, Daban karfe, Daban Gajere, Tumbin Buhari da Tumbin Abuja. Sauran sune Sabon Tumbi, Ali Sherifti, Doron Nairada Daban masara.

Babban Kwamandan MNJTF Janar AK IBRAHIM

A dai sansanin 'yan ta'addan sojojin sun sami katan katan na bandar kifi Gero da sauran kayayyakin amfanin gona, babura da wata tsohuwar akori kura, dakarun kazalika sun cafke wasu mutane talatin da suke ikirarin su fa masunta da manoma ne, al'amarin da yasa tuni aka kaddamar da bincike akansu,

A baya bayanna dai rundunar kasashen tafkin Chadin ta kaddamar da wani mummunan farmaki mai take OPERATION LAKE SANITY inda ta karkashe dimbin 'yan ta'addan Boko Haram da ISWAP, wasu kuma aka kashe yayin da karin wasu kuma su ka yi saranda irinsu Qatada dan asalin kasar Nijar da yace lalle kam sun sha wulakanci a sansanin yan ta'addan, abin ma ke nan da yasa ya mika wuya

Rundunar hadin guiwa a yankin Tafkin Chadi

Duk da haka babban kwamandan dakarun kasashen yankin tafkin Chadin, Janar AK Ibrahim ya ce ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen ganin sun kara ninka kokarin tabbatar da zaman lafiya a yankin baki daya.

A daya bangaren kuma dakarun tafkin Chadin sun sake kaddamar da wani sabon aikin kammala kakkabe yan ta'addan daga bangaren Malamfatori ta bangaren Najeriya har zuwa yankin Diffa a bangaren Nijar ta wajajen Aji Jimari, Dogon Chuku da Tumbin Rago.

Sansanin 'yan ISWAP

Ko a baya sai da wani basarake a yankin Diffa Mai martaba Sarkin Kanton Kingimi Mai Inusa Mai Manga ya yi wa muryar Amurka karin bayani kan irin wahalhalun da ta'asar Boko haram ta haifar masu musamman da ya ke kasarsa na dab da tafkin Chadin.

Saurari cikakken rahoton Hassan Maina Kaina cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Dakarun hadin guiwa a yankin Tafkin Chadi sun kai harin kakkabe 'yan ta'addan-3:00"