Dakarun Iraqi Sun Kwato Birnin Fallujah Gaba Daya daga Hannun Mayakan ISIS

Dakarun Iraqi suna suntiri bayan da suka gama kwato birnin Fallujah

Bayan sun yi fiye da makonni hudu suna yaki ba dare da rana a Fallujah yanzu darakun Iraqi da taimakon kawancen da Amurka ke jagoranta sun kwato birnin Fallujah bayan sun kakkabe duk mayakan sakan ISIS.

A Iraqi dakarun kasar sun kwato birnin Fallujah daga hanun mayakan sakan ISIS, bayan da suka kaddamar da farmaki na tsawon wata daya, kamar yadda wani babban jami'in kasar yayi bayani.

Jiya Lahadi Leftanar Janar Abdul-wahab al-Sa'adi yace "yanzu an 'yanto Fallujah baki daya" bayanda sojojin kasar suka kama unguwar da ake kira Julan, wacce itace ta karshe da ta rage a hanun mayakan sakan na ISIS.

An yiwa binrin mumunar barna.

Tareda goyon bayan rundunar taron dangi da Amurka take yiwa jagoranci wacce take barin wuta da jiragen yaki, da kuma tawagar mayakan sakai na 'yan shi'a, sojojin Iraqi sun yi yaki gadan gadan na makonni domin fatattakar 'yan ISIS. Babu rahoto kan adadin mayakan sakai da sojojin Iraqi da suka mutu ko suka jikkata a gumurzun da aka yi domin kwato birnin na Fallujah.