Dakarun Iraqi Sun Fara Kai Farmaki Kan Mayakan ISIS Daga Arewacin Birnin Mosul

Dakarun Iraqi.

A Iraqi dakarun kasar wadanda suke samun goyon bayan Amurka sun fara farmaki da zummar tusa keyar mayakan sakai na ISIS daga arewacin birnin Mosul, mataki na baya bayan nan a farmakin da aka fara watanni hudu da suka wuce domin kwato birnin wanda shine na biyu a girma a kasar.

"Dakarunmu suna fara aikin 'yanto 'yan kasa daga kungiyr Deash, inkiyar kungiyar da harshen larabci," inji Fara Ministan kasar Haider al-Abadi, wanda ya bayyana haka jiya Lahadi.

Sojojin Iraqi sun kwato kauyuka masu yawa a zaman wani bangare na sabon matakin sojan d a suka dauka, yanzu sunyi harama kan tashar jirgin sama na birnin Mosul din.

Sakataren tsaron Amurka Jim Mattis, ya fada jiya Lahadi cewa, sojojin Amurka za su ci gaba da aiki kamar yadda suke yi tunda farko.

Sai dai MDD tana gargadin cewa dubun dubatan mutane a Mosul suna fuskantar hadari.