Kungiyar ta yi zaman tattaunawa masu yawa da yan majalisu wanda ya kara mai da kai kan kokarin Donald Trump na hana baki daga wasu manyan kasashen bakwai shigowa Amurka.
Burin 'yan kungiyar ta Ahmadiyya a Amurka shine su tattauna kan 'yancin aiwatar addini da 'yancin Dan Adam da tsaron kasa da kuma kara mai da kai kan yada manufa da sako na cewar mafiya yawan musulmai masu son zaman lafiya ne.
Dan majalisa Jim McGovern na jam’iyyar Demokrat ya fada wa muryar Amurka a wata tattaunawa cewar, “Tuni wannan kungiya tana aiki da Amurka domin rushe rashin sanin da ke yawo akan addinin Islama. Ya kara da cewa wannan kungiya ce mai muhimmanci ga al’umma, wacce take kokarin tabbatar da zaman lafiya da kuma kawar da tashe-tashen hankula da zama irin na kauna.”
An shirya zaman tattaunawar ne tsakanin shugabannin kungiyar zango na 75 da 'yan majalisu kimanin 100, inda suka gabatar da jerin bayanai a gaban wani allo da aka rubuta “Addinin Islama Gaba Daya Yayi Allah Wadai Da Ayyukan Ta’addanci”.
Aka kuma kara da rubutun ayoyin Qur'ani mai girma domin kafa hujjar abinda aka rubutan. Amjad Khan daya daga cikin 'ya'yan kungiyar ya fadawa Muryar Amurka cewa “Ba zamu bari labaran da ake bayar wa marar sa kyau su zama sune kadai ake jiba.”
Facebook Forum