Dakarun Iraqi na fuskantar tirjiya a kokarin kwato Mosul daga mayakan ISIS

Ministan tsaron Iraqi a tsakiyan sojoji biyu Khaled al-Obeidi

Kokarin da dakarun Iraqi ke yi domin sake kwato birnin Mosul daga hannun mayakan ISIS na fuskantar trijiya.

Dakarun Iraki na fuskantar tirjiyar a wani yunkurin farko da suka fara da karfe 6 na safiyar jiya Alhamis, da nufin sake kwato ikon babbar ‘yan ISIS, wato birnin Mosul da suka kwace ikon garin. Kimanin sojojin Iraki 4000 ne suka kutsa kauyakun dake makwabtaka da Mosul da tazarar akalla kilomita 75 daga Kudu maso Yammacin kasar.

Dakarun Pershmerga sun ce yanzu haka ma har an kwato wasu kauyukan a yankin. Ratoton da Muryar Amurka ta kalato kai tsaye daga filin dagar yace, Sojojin sun rabu gida 2 ne suka yiwa kauyakun kofar rago, kafin 12 na rana tuni har sun kwace kauyaku 4 amma har yanzu da sauran wasu.

Kamar yadda shugaban sojojin na Peshmerga Janar Najat Ali ya fadawa Muryar Amurka. Ya kara da cewa, a yanzu haka dai Sojojin Irakin sun dan daga kafa da kutsawa saboda canza salo, domin kuwa ‘yan ISIS din sun fuskancesu da muggan makamai da ‘yan kunar bakin wake ba ji ba gani a yanki da suke kira da babban birninsu.

Yawancin dai sojojin na Peshmerga ‘yan bangaren Sunni ne da ke runduna ta 15 da suka sami horo daga sojin Amurka. To amma Janar Najat yace suna nan a ankare da wajen tare da sa idanu wajen fuskantar ‘yan ta’addar na ISIS.