Dakarun Iran Sun Kashe 'Yan ta’adda A Yankin Kudu Maso Gabashin Kasar

Birnin Tehran na Iran

Sojojin Iran sun kashe akalla ‘yan ta’adda hudu a kudu maso gabashin kasar a ranar Lahadi bayan wani kazamin harin da ‘yan ta’adda suka kai wa ‘yan sanda a ranar Asabar.

Akalla jami’an ‘yan sanda 10 ne suka mutu a harin, daya daga cikin mafi muni da kungiyar masu da’awar jihadi ta dauki alhakin kai wa a yankin kan iyaka tsakanin Pakistan da Afghanistan.

An kai harin ne kan motocin 'yan sanda a gundumar Taftan, wani yanki na Sistan da Baluchestan, yanki mai tazarar kilomita 1,200 daga Tehran babban birnin kasar.

Kungiyar 'yan jihadi ta Sunni Jaish al-Adl da ke Pakistan da ke aiki a yankin, ta dauki alhakin kai harin ta hanyar aika sakon Telegram.

A cewar kamfanin dillancin labarai na Tasnim, jami'an tsaro sun kashe akalla hudu daga cikin “'yan ta'addan” da ke da hannu a harin a wani harin da aka kai da jirgin sama mara matuki.

Sistan da Baluchestan, wadanda ke da iyaka da Pakistan da Afganistan mai tsayi, na daya daga cikin yankuna mafi talauci a Iran.

Yankin dai na da dumbin al'ummar kabilar Baloch, wadanda ke bin addinin Sunni, sabanin reshen Shi'a da ke da rinjaye a kasar.

Rikicin da ake ci gaba da gwabzawa a can ana fafatawa tsakanin jami'an tsaron Iran da 'yan tawaye daga kabilar Baluch marasa rinjaye, da kungiyoyin 'yan Sunni masu tsattsauran ra'ayi, da masu safarar muggan kwayoyi.