Bakin haure sama da 80 da ke cikin jirgin ruwan nan na kasar Spain da ya cecesu a kan teku, sun taka doron kasa a karon farko, bayan da suka kwashe kwanaki 20 a cikin jirgin da ya yi ta galantoyi akan teku.
WASHINGTON DC —
Lamarin ya faru ne bayan da hukumomin Italiya suka kwace jirgin mai suna “Open Arms” wanda ke ayyukan jinkai na kubutar da bakin hauren da su ka makale akan teku.
Andre Mahecic, shi ne kakakin hukumar da ke kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, ya kuma ce “Akwai bukatar a tallafa musu, domin ganin sun koma cikin hayyacinsu, saboda an ci zarafin aksarinsu cikin watannin da suka kwashe a kasar Libya.”
Bakin hauren dai sun barke da shewa, a lokacin da suka ji labarin cewa hukumomin Italiya sun kwace jirgin.