A yau Talata, Rasha ta soki Amurka game da gwajin wani makami mai linzami wanda har zuwa makwanni uku da suka gabata an haramta shi a karkashin yarjejeniyar makamai tsakanin kasashen biyu.
Ministan harakokin wajen Rasha, Sergei Ryabkov ya zargi Amurka da cewa ta “zabi matakin neman tsokano zaman dar-dar na soja tsakaninta da Rasha”, har ya kara da cewa ba za a shigar da Rasha cikin "tseren makamai ba."
Kalamin nasa ya zo ne kwana guda bayan da Pentagon ta ba da tabaccin cewa Amurka tayi gwajin.
A ranar Lahadi ne aka harba wannan makami mai linzami a tsibirin San Nicolas, dake jihar California ta nan Amurka¸inda kuma hukumomi suka ce an cimma biyan bukatar da aka so, don gwajin"ya yi tasiri sosai bayan yayi tafiyan sama da adadin kilomita 500 cikin sararin samaniya."
Facebook Forum