Wannan shi ne karon farko da shugaban kasa zai gabatar da daftarin kasafin kudi, ba tare da kasafta shi ga bangarori daban- daban da za a yi aiki kan su ba.
Alal misali, Bola Ahmed Tinubu bai ce an ware wasu kudade ga bangaren ilimi ko kiwon lafiya, ko noma ko hanyoyi da sauran su ba.
Abin da ya yi, shi ne bayyana abin da za a ware wa banagaren manyan aiyuka, da aiyukan yau da kullum da kuma ko a nawa ne za a sayar da gangan danyen man fetur a Kasuwar duniya da kuma ko kan Naira nawa ne za a canza dalar Amurka daya.
Shugaba Tinubu ya ce ministan mai kula da kasafin kudi zai kawo bayanan da daftarin ya kamata ya kunsa daga baya, wani abu da Yusuf Shittu Galambi dan Jamiyyar NNPP daga Jihar Jigawa, ya baiyana shi da yaudara.
Galambi ya ce kamata ya yi a kawo wa Majalisa kasafin kudin tun watan tara, domin a samu a kammala aiki akai, saboda a fara aiwatar da kasafin a watan farko na shekara 2024.
Ya kara da cewa Majalisa za ta yi iya kokarinta a gani, idan zai yi wu su kammala aiki kan kasafin zuwa karshen wannan shekara, amma yana ganin abin na da kamar wuya.
Amma ga shugaban kwamitin kula da kasafin kudi a Majalisar Wakilai Abubakar Bichi, cewa ya yi kasafin da shugaba Tinubu ya gabatar kasafi ne da zai amfani Jama'a.
Da yake bayani kan batun ciwo bashi da aka ce za a yi domin cike gibin kasafin kudin, kwararre a fanin tattalin arziki Dokta Sa'ad Usman, ya yi gargadi kan batun ya na cewa akwai alamun ana bin Najeriya dimbin bashi ya zuwa yanzu.
Sa'ad ya ce idan an duba kasashen da suka ci gaba ma suna ciwo bashi, sai dai abin dubawa shi ne Najeriya ta sani cewa za ta biya basussukan da ake bin kasar har da kudin ruwa da aka dora, saboda haka a rika sara ana duban bakin gatari.
Majalisa ta ce za ta ci gaba da zama har ranakun Asabar da Lahadi idan ta kama, domin a samu a kammala aiki kan kasafin kudin.
Saurari rahotan Medina Dauda:
Your browser doesn’t support HTML5